in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira da a warware rikicin Kenya cikin ruwan sanyi gabanin sabon zaben da za a yi
2017-10-05 12:25:02 cri
Tarayyar Afrika AU, ta yi kira da a warware rikicin Kenya cikin ruwan sanyi, gabanin sabon zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa ranar 26 ga wannan watan.

Sanarwar da AU ta fitar a jiya Laraba, ta ce Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat na ci gaba da bibiyar yadda batun siyasar kasar na baya bayan nan ke tafiya cike da damuwa, biyo bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke da ya soke zaben ranar 8 ga watan Augustan bana da aka yi tare da sanya sabon ranar gudanar da zaben da aka yi.

Moussa Faki Mahamat, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su kauracewa yin duk wani abu ko furuci da zai iya haifar da koma baya ga tsarin demokradiyyar kasar ko zubar da nagartar zaben da aka shirya gudanarwa ko kuma kawo tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, wadanda ya ce ka iya haifar da mummunan tasiri ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki su yi aiki da hukumar zaben kasar domin tabbatar da an gudanar da sabon zaben kamar yadda aka shirya, tare da kauracewa daukar wani mataki ko furuci da ka iya shafar 'yancin cin gashin kai na hukumar zaben. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China