in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a Iraki
2017-10-27 09:55:19 cri
Kwamitin sulhun MDD ya bayyana damuwa matuka game da yadda ake samun rahotannin karuwar zaman tankiya da tashin hankali tsakanin sojojin gwamnatin Iraki da mayakan Kurdawa.

Jakadan kasar Faransa a MDD kana shugaban kwamitin sulhu na wannan wata Francois Delattre wanda ya bayyana hakan, yayin zaman kwamitin ya ce daukacin mambobin kwamitin sulhun MDDr sun bukaci bangarorin da abin ya shafa, da su koma kan teburin sulhu a matsayin hanya mafi dacewa ta hana barkewar duk wani tashin hankali a kasar, maimakon amfani da karfi ko barazana.

A cewar mambobin kwamitin sulhun, muddin ana bukatar a kare 'yanci da hadin kan kasar Iraki, to wajibi ne a dauki matakan da suka dace na yakar kungiyar IS.

Rahotanni na cewa, zaman dar-dar na karuwa tsakanin mahukuntan kasar Iraki da yankin Kurdistan, tun bayan da Kurdawan kasar ta Iraki suka gudanar da kuri'ar raba gardama game da neman ballewar yankin da ma wasu yankuna da ake takaddama a kansu. Wannan ya sa dakarun Iraki suka daura damarar sake kwace yankin dake karkashin ikon Kurdawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China