An dage zaben majalisar dokoki da na shugaban yankin Kurdistan na kasar Iraki
Hukumar zaben koli da na jin ra'ayoyin jama'a ta yankin Kurdistan na kasar Iraki, ta bayar da sanarwa a ranar 18 ga wata, inda ta bayyana cewa, sakamakon hali mai tsanani a jihar Kirkuk da fuskantar matsalar rajistar 'yan takara masu halartar zaben, an dakatar da shirya zaben majalisar dokoki da na shugaban yankin Kurdistan da aka shirya yin su a ranar 1 ga watan Nuwamba, don haka an jinkirtar da jefa kuri'u a zaben har zuwa lokacin da majalisar dokokin yankin ta tsaida sabon kuduri kan batun zaben. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku