Gidan telebijin na kasar ya ruwaito cewa, bisa umurnin firaministan, tuni aka jibge sojojin gwamnatin kasar, ciki har da sojojin yaki da ta'addanci da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a wasu yankunan dake jihar Kirkuk.
Babu kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin jihar Kirkuk da gwamnatin tsakiya ta kasar Iraki, kuma dakarun Kurdistan sun mallaki wasu yankuna, ciki har da jihar Kirkuk wadda ke fuskantar matsalar ikon mallaka, inda aka yi wa yankunan lakabi da "yankunan rikici".
Manazarta sun yi hasashen cewa, idan sojojin gwamnatin tsakiya na kasar suka shiga yankin ba tare da samun izni ba, zai iya haifar da rikici. (Zainab)