Cikin mintoci 13 kachal da fara wasan, Abel Ruiz ya budewa Spaniya da zara kwallon farko.
Dan wasan kungiyar mai amfani da kafar hagu Sergio Gomez, ya samu nasarar zara kwallo ta biyu a wani bugu da yayi daga waje mai nisa.
Mintoci 7 bayan kwallon ta biyu, Ferran Torres ya kara kwallo ta uku.
Saeid Karim shine ya zarawa Iran kwallo mintoci 69 da fara wasan, sai dai hakan bai wadatar ba.
Iran ta samu nasarori har guda hudu da suka hada da Guinea da ci (3-1), sai Jamus da ci (4-0), da Costa Rica da ci (3-0) da kuma Mexico da ci (2-1).(Ahmad Fagam)