Jorge Celico ya bayyana hakan ne, bayan da suka buga wasanin su na rukuni da tarin kalubale. Yanzu haka dai kungiyar ta Ecuador ita ce ta 8 a rukunin kungiyoyin kasashen kudancin Amuka ko CONMEBOL, kuma ya zamewa kungiyar wajibi ta lashe wasannin ta na neman gurbin guda 2, na daya da kungiyar kasar Chile a ranar 5 ga watan Oktoba, dayan kuma a gida da Argentina kwanaki 5 bayan wasan na farko.
Koci Celico ya ce yana da 'yan wasa masu kwazo, abun da kawai suke bukata shi ne hada karfi wuri guda, domin ganin sun lashe wasannin 2 na gaba.
Ecuador dai ta sallami tsohon kocin ta Gustavo Quintero. Koci Celico ya kuma ce bai gamsu da uzurin da tsohon kocin kungiyar Quintero ba, na cewa 'yan wasan sa sun gaza cimma nasarar wasannin su na baya ne, sakamakon tudun filin wasan da suka taka leda a cikin sa a birnin Quito.
An ce filin wasan ya kai tudun mita 2,700 daga doron kasa. Ya ce duk da hakan ba zai hana 'yan wasan samun nasara ba.
Kungiyoyi 4 dake rukunin mafiya hazaka ne dai zasu wakilci rukunin, a gasar cin kofin duniyar da za ta gudana badi a kasar Rasha, yayin da ta 5 za ta kara da wata kungiyar wajen nahiyar domin samun gurbi.(Saminu Alhassan)