in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakamakon wasan share fagen gasar cin kofin duniya na 2018
2017-10-12 13:49:42 cri

Masar ta samu tikitin halartar gasar cin kofin duniya ta 2018

Bayan shekaru fiye da 20, kasar Masar ta sake samun tikitin halartar gasar cin kofin duniya wadda za a gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018 bayan da ta doke kasar Congo da ci 2 da 1 a wasan da aka gudanar a birnin Alexandria a kwanakin baya.

Kasar Masar ta zama kasa ta biyu bayan kasar Nijeriya da ta samu damar halartar gasar cin kofin duniya da za a gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018. Wannan ne karo na 3 da kasar Masar ta samu damar halartar wannan gasa, bayan shekarar 1990 da na 1934.

Mashahurin dan wasan kasar Masar Mohamed Salah wanda ke taka lada a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kasar Ingila, shi ne gwarzon dan wasa a wannan wasa, inda ya zura dukkan kwallaye biyu a raga a minti na 63 da na 93. (Zainab)

Kasar Ingiya ta doke Lithuania a wasan neman zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018

A ranar Lahadin da ta gabata ne, kasar Ingila ta doke kasar Lituania da ci daya da nema a wasan rukunin F na neman zuwa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018.

An gudanar da wasan ne a filin wasa na LFF dake birnin Vilnius dake kasar Lithuania.

Bayan da kasar Ingila ta yi nasara a wannan wasan, ta samu maki 26 kana ta kasance a matsayi na farko a rukunin F, hakan ta ba ta damar samun tikitin halartar gasar da za a buga a Rasha a shekarar 2018, yayin da kasar Lithuania ta kasance a matsayi na biyar a rukunin da maki 6.

Za a gudanar da gasar cin kofin duniya a kasar Rasha tun daga ranar 14 ga watan Yuni zuwa ranar 15 ga watan Yuli na shekarar 2018. Kasar Rasha ma ta samu iznin halartar gasar kasancewarta mai daukar bakuncin gasar, saura kasashe 31 suna kokarin samun tikitin halartar gasar. (Zainab)

Ghana ta tashi kunnen doki da Uganda a wasan share fagen shiga gasar kofin duniya ta FIFA

Kungiyar wasan Black Stars ta kasar Ghana ta yi canjaras da takwararta ta kasar Uganda a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2018 wanda suka gudanar da wasan a ranar Asabar.

Kunnen dokin da kungiyoyin biyu suka yi a wasan, ya karawa Ghana kwarin gwiwa na yiwuwar samun nasarar shiga gasar cin kofin duniyar a kasar Rasha, koda yake itama Uganda a baya tayi ta addu'ar ganin Congo Brazzaville ta lallasa Masar a wasan da suka buga a ranar Lahadi.

Dan wasan gaba na kungiyar wasan Ghana Emmanuel Arnold Okwi, shine ya jagoranci kara kaimi ga masu tsaron baya na kungiyar wasan ta Ghana.

Farouk Miya ya hambarar da bugun da aka yi na free kick bayan mintoci 6 da fara wasan, yayin da Okwi ya fara gwada sa'arsa mintoci 17 bayan fara wasan inda ya kubutar da Richard Ofori mai tsaron ragar Ghana.

Bayan mintoci 34 da fara wasan, Daniel Opare ya kusa ya samarwa Ghanan wata dama, sai dai bai yi nasarar zara kwallon ba.

A zagaye na biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Ghana ta samu nutsuwa a wasan, sai dai bata samu gwarzon dan wasan da zai zura mata kwallaye a ragar abokiyar karawar tata ba. Kociyan kungiyar wasan Ghana Kwesi Appiah, ya gudanar da wasu 'yan sauye sauye, amma duk da hakan 'yan wasan nasa basu samu zarafin doke kungiyar wasan ta Uganda ba.

Daniel Nsibambi ya kusa ya tonawa Ugandan asiri, amma mai tsaron ragarta yayi nasarar kadar da kwallon wanda Geoffrey Walusimbi yayi mummunan bugu.

Dan wasan Uganda William Kizito Luwagga, ya samu rauni yayin da aka dawo wasan bayan hutun rabin lokaci.

Yayin da ya rage mintoci da aka kara a wasan, Okwi yayi ta yunkurin zara kwallon amma mai tsaron ragar Ghanan ya dakile yunkurin dan wasan.

Duk da kasancewar Ghana ta sauya dan wasanta inda ta maye gurbinsa da Patrick Twumasi, amma duk da hakan hakarta bata cimma ruwa ba. Yan wasan Ghana sun yiwa jami'an gudanar da wasan kawanya bayan an hura usur na karshen wasan.

Jim kadan da kammala wasan, kociyan kasar Uganda Moses Basena ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sun gamu da takaici, kasancewar sun gaza samun maki uku wanda shine zai basu damar lashe wasan.

Shikuwa Appiah kociyan Ghana, na nuna bacin ransa ne, kasancewa alkalin wasan dan kasar Afrika ta kudu ya soke kwallo guda wanda kungiyar wasansa ta zura, inda ya bayyana kwallon da aka zara din da cewar mai kyauce.

Kunnen dokin da aka samu a wasan ya daga likafar kungiyar wasan Masar zuwa rukunin E da maki 9, inda Uganda ta daga da maki 8, yayin da Ghana ta tashi da maki 6. (Ahmad Fagam)

Jamus ta lallasa Azerbaijan da ci 5-1 a wasan share fagen cin kofin duniya

A cigaba da fafatawar da ake na neman shiga gasar cin kofin duniya, kungiyar wasan kwallon kafa ta Jamus ta yi nasara a wasansu na 10 bayan da suka doke Azerbaijan da ci 5-1 a wasan karshe na rukunin C na share fagen shiga gasar cin kofin duniya wanda aka gudanar a ranar Lahadi.

A halin yanzu Jamus ta samu nasarar kaiwa matakin karshe na shiga gasar cin kofin duniyar na shekarar 2018 a kasar Rasha, bayan da dan wasan kungiyar Leon Goretzka ya taimakawa kungiyar ta doke Azerbaijan mai masaukin baki da ci 5-1 a Kaiserslautern.

Da farko dai mai masaukin bakin ta fara wasan ne da kafar dama, bayan wasu jerin hare hare data dinga kaiwa kafin daga bisani dan wasan na Jamus Goretzka ya samu nasarar zara kwallo mintoci 8 da fara wasan a wani bugun gefe da aka gudanar.

Yan wasan Joachim Loew, sun yi kusan sake zara kwallo ta biyu a mintoci 30 da fara wasan, sai dai dan wasan kungiyar Sandro Wagner ya nuna damuwa sakamakon barar da kwallon da suka yi a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Azerbaijan ta mayar da martani inda ta baiwa mai masaukin bakin mamakin bayan da suka yi kunne doki bayan dan wasanta Ramil Sheidaev, ya zara kwallonsa wadda ta gagari Bernd Leno mai tsaron ragar ta Jamus lamarin da ya basu damar yin kunnen doki wato 1-1 kafin zuwa dan wani lokaci.

Sai dai daga bisani kunnen dokin da aka samu ya sauya, a yayin da Joachim Loewy ya bukaci hutun rabin lokaci don nunawa 'yan wasansa kura-kuransu. Dan wasan Jamus Sandro Wagner, shine ya mayar da kwallon ta koma 2-1 bayan da yayi amfani da bugun da Julian Brandt yayi mintoci 54 da fara wasan.

Jamus ta kara matsawa gaba mintoci 10 bayan zura kwallonta ta biyu a lokacin da Antonio Ruediger yayi yunkurin buga kwallon, kafin daga bisani Goretzka ya tallafa masa ya zura kwallon cikin ragar Leroy Sane mintoci 66 da fara wasan.

Azerbaijan bata samu nasarar dakile hare haren da ake kaimata ba, yayin da Jamus ta cigaba da kokarin kara yawan kwallayenta har aka tashi ci 5-1.

Jamus ta samu babban matsayi inda ta tashi da maki 10 a rukukin C, sai Northern Ireland dake bi mata baya da maki (19 points), Czech Republic da maki (15 points), Norway da maki (13 points), Azerbaijan da maki (10 points) sai kuma San Marino ba tare da maki koda guda ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China