in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guangzhou Evergrande ta lashe kofin CSL na 7 a jere
2017-10-25 21:24:27 cri
Kungiyar kwallon kafa ta Guangzhou Evergrande, ta lashe kofin gasar zakarun kulaflika ta kasar Sin CSL karo na 7 a jere, gabanin ma ta kammala sauran wasannin ta biyu na kakar bana. Kungiyar ta cimma wannan nasara ne bayan da ta doke takwarar ta ta Guizhou Hengfeng da ci 5 da 1, a wasan mako na 28 da suka buga a Lahadin karshen mako.

Dan wasan kungiyar Gao Lin, ya jefa kwallon sa ta 100,cikin minti na 15 da take kwallo. Kaza lika Alan ya kara kwallo ta biyu a ragar Guizhou Hengfeng mintuna 2 bayan kwallon farko.

Dan lokaci bayan kwallon biyu a ragar Guizhou Hengfeng, sai Wang Fan ya ciwa Guizhou kwallon su ta farko, sai dai ba da jimawa ba kuma sai dan wasan kungiyar Du Wei ya ci gida, wanda hakan ya sanya tazarar su da Guangzhou Evergrande ta fadada.

Gabanin tashi daga wasan ne kuma Yu Hanchao, da Muriqui suka kara kwallaye daya daya a ragar Guizhou Hengfeng, haka kuma aka tashi Evergrande na da kwallaye 5 Guzhou na da 1.

A daya hannun kuma kungiyar Shanghai SIPG dake matsayi na biyu a teburin gasar da maki 9, kasa da Guangzhou Evergrande, ta yi rashin nasara a hannun Guangzhou R&F a gida, inda suka tashi wasan su na karshen mako, Shanghai SIPG na da kwallo 1 Guangzhou R&F na da kwallo 2. Ita ma dai kungiyar Shanghai SIPG na da ragowar wasanni biyu kafin karkare wannan gasa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China