in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dembele zai yi jiyyar watanni 3 zuwa 4 jim kadan bayan komawar sa Barcelona
2017-09-21 09:27:18 cri
Kungiyar kwallon kafar Barcelona za ta shafe watanni 3 zuwa 4 ba tare da sabon dan wasan gaban ta Ousmane Dembele ba, bayan da dan wasan ya ji rauni wasanni 3 kacal da fara bugawa kungiyar kwallo a wasan kungiyar da Getafe, wasan da aka tashi Barcelona na da kwallo 2 Getafe na da 1, a wasan ranar Asabar din karshen mako.

Dembele ya koma Barcelona, bayan da kungiyar ya sayo shi kan kudi har Euro miliyan 140 daga kungiyar Borussia Dortmund. Ya kuma samu rauni a wasan karshen mako, bayan fara taka leda tsawon mintuna 26 da take wasa.

Tuni dai kungiyar Barcelona ta fidda sanarwa, wadda ta bayyana cewa Dembele ya ji ciwo ne a agarar sa, zai kuma tafi Finland domin jiyya, kuma ga dukkanin alamu ba zai sake taka leda ba har sai sabuwar shekara, matakin da zai zamo babban kalubale ga kungiyar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China