Kungiyar kwallon kafar ta mata ta kasar Brazil ta sauka zuwa matsayi na 9 a jadawalin kungiyoyin kasashen duniya mafiya kwarewa wajen murza leda, wanda hukumar FIFA ke fitarwa. Amma duk da haka, sun mamaye gasar da yanzu haka ake bugawa ta kasashe 4, inda ta samu nasara a wasannin ta biyu na baya bayan nan a biranen Yongchuan, da Chongqing, dake nan kasar Sin.
Da take tsokaci game da hakan, Marta ta ce dama dai kwallon kafa haka ta gada. Wasu lokutan nasara wasu lokutan kuma rashin ta. Marta na tsokacin ne bayan da ta jefa kwallo a wasan ranar Lahadi, wanda aka tashi Brazil na da kwallo 2 Koriya ta kudu na nema, a zagaye na biyu na gasar. Ta ce sun sha fama da kalubale daban daban, amma yanzu kungiyar su na neman dabarun farfadowa, kuma ko shakka ba bu, za su sake komawa matsayin su na gwanaye a harkar taka leda.
Yanzu haka dai koci Oswaldo Fumeiro Alavarez ne ke jagorantar kungiyar ta Brazil, duk da cewa aikin na sa ya hadu da cikas, lamarin da ya sanya wasu daga masu takawa kungiyar kwallo ayyana sallama da kungiyar. Wannan ne kuma karo na biyu da yake jagorantar kungiyar ta Brazil, bayan da a baya, ya samu nasara tare da kungiyar a gasar Olympic ta birnin Rio.
Game da wannan danbarwa, Marta ta ce dukkanin 'yan wasan kungiyar na da matukar muhimmanci, kuma ba za a yi fatan wata daga cikin su ta kauracewa kungiyar ba. Kaza lika tana fatan wadanda suka yiwa kungiyar yaji da su dawo domin a ci gaba da wasa tare da su.
A dai wannan gasa da ake bugawa, Marta ta zura kwallaye 3 a ragar abokan hamayya, ciki hadda wadda ta jefa a ragar Mexico, a wasan da aka tashi Brazil na da kwallo 3 Mexico na nema.
Gabanin wasan da kungiyar za ta buga da kasar Sin. Marta ta ce wasan ta na karshe da kasar Sin shi ne wanda suka buga a gasar cin kofin duniya na shekarar 2007. Ta ce tana iya tuna yadda 'yan wasan Sin suka taka rawar gani sosai a wannan gasa. Kana sun nuna kwarewa a gasar Olympics ta 2008. (Saminu Alhassan)