in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban Bankin Nijeriya ya zuba dala miliyan 195 cikin kasuwar musayar kudi
2017-10-25 14:15:45 cri
Babban bankin Nijeriya CBN ya ce ya zuba dala miliyan 195 cikin kasuwar musayar kudaden ketare.

Sanarwar da kakakin Bankin Isaac Okorafor ya fitar, ta ce bankin ya bada dala miliyan 100 ga bangaren dilalan da hukumar ta amince da su.

Ya ce bangaren kanana da matsakaita sana'o'i kuwa ya samu dala miliyan 50, yayin da wadanda ke bukatar canji domin biyan kudin makaranta da na asibiti da kudin guzuri da dai sauransu, suka samu dala miliyan 45.

A cewar Isaac Okorafor, CBN na da tabbacin cewa, gaskiyar da ya tsare a kasuwar, za ta taimakawa takardar Naira rike darajarta a kan dala, tare da kara mata karfi a kan sauran manyan takardun kudaden na duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China