in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya za ta rufe asusun ajiyar bankunan da ba su da lambar BVN
2017-10-24 09:54:38 cri
Rahotannin daga Najeriya na cewa, mahukuntan kasar na shirin rufe dukkan asusun ajiyar bankunan da ba su da lambobin tantancewa na BVN, a wani mataki na yaki da masu halatta kudaden haram.

Yanzu haka babbar kotun tarayyar kasar da ke Abuja, fadar mulkin kasar ta umarci babban bankin kasar CBN da wasu bankunan kasuwanci 19 dake kasar, da su bayar da bayanan irin wadannan asusun ajiya da suke mu'amala da su, wadanda suka mallake su da kudaden da ke ciki.

Haka kuma kotun ta umarci bankunan da su rufe wadannan asusun ajiya na dan wani lokaci kafin a sanar da gwamnatin yawan kudaden da ke cikin wadannan asusun ajiya.

Wasu daga cikin bankuan dai sun fara nuna aniyarsu ta bayar da hadin kai, muddin ba su samu wani umarni daga kotu game da dakatar da wannan shiri cikin wa'adin da aka bayar ba.

Mai magana da yawun bankin Unity, Matthew Obiazikwo, ya ce yanzu haka bankinsu ya rufe irin wadannan asusun ajiyar da ba su da lambobin na BVN, kuma da zarar bankin ya samu izni daga kotu zai wallafa sunayen masu asusun.

Su ma bankunan Guaranty Trust da Heritage da UBA, sun nuna aniyar su ta martaba umarnin kotun. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China