in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya kori wani babban jami'in Gwamnatinsa bisa zargin cin hanci
2017-10-24 10:55:37 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bada umarnin korar Abdurrasheed Maina, wani babban jami'in Gwamnatinsa da ake zargi na da hannu cikin badakalar cin hanci da rashawa.

Umarnin na Shugaban kasar ya biyo bayan suka da kiraye-kirayen neman korar babban jami'in da a baya-bayan nan, aka sauyawa wajen aiki zuwa ma'aikatar kula da harkokin cikin gida bisa wasu batutuwa masu sarkakiya.

Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya, Muhammadu Buhari ya nemi a gabatar masa da cikakken rahoto game da mayar da Jami'in bakin aiki tare da tura shi ma'aikatar harkokin cikin gida a matsayin mukaddashin Darakta.

Abdurrasheed Maina ya taba shugabantar kwamitin kar ta kwana na fadar Shugaban kasa kan yiwa tsarin fansho garambawul. Kuma yayin da ya ke rike da mukamin, an yi zargin ya karkatar da akalar wasu kudi Naira biliyan 100, kwatankwacin dala biliyan 278 na kudin fansho da hadin bakin wasu.

Hukumar yaki da masu yi tattalin arzikin kasar zagon kasa wato EFCC, ta gurfanar da shi gaban kotu a shekarar 2015 duk da cewa baya nan.

Haka kuma, a cikin shekarar ne hukumar kula da ma'aikata ta kasar ta kore shi bisa rashin zuwa aiki.

Bugu da kari, a makon da ya gabata hukumar ta EFCC ta ce har yanzu Abdulrasheed Maina na cikin jerin wadanda take nema. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China