in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar adawa a Najeriya ta lashi takobin kwace mulki a 2019
2017-10-19 09:50:18 cri
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta ce a halin yanzu ta dawo da karfinta, kuma a shirye take ta kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC mai mulkin kasar a shekarar 2019.

Godwill Akpabio, wani kusa ne a jam'iyyar ta PDP, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja fadar mulkin kasar bayan kammala taron kusoshin jam'iyyar.

Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom mai arzikin mai ne, ya bayyana cewa, mafi yawa daga cikin magoya bayan sauran jam'iyyun siyasar kasar sun amince za su marawa babbar jam'iyyar adawar baya.

Dan siyasar wanda a halin yanzu yana daga cikin manyan dattawan jam'iyyar ya ce, ya nazarci halin da jam'iyyar ke ciki a dukkannin jihohi, kuma ya gano cewar jam'iyyar ta samu matukar karfi fiye da yadda take a lokacin baya.

Ya ce yana bukatar shugabancin jam'iyyar na kasa ya bude kofa don karbar kowa da kowa tun daga yanzu har zuwa lokacin babban taron jam'iyyar.

Akpabio, ya bayyana cewa kusoshin jam'iyyar sun tattauna game da ka'idojin da za'a bi wajen aiwatar da babban taron jam'iyyar domin bada kyakkyawar gudunmowa a taron kwamitin zartaswar jam'iyyar.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel, dake kudu maso yammacin kasar, ya nuna aniyarsa na tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar na kasa.

A cewar Daniel, babban burinsa shi ne ya tabbatar jam'iyyar ta samu nasara a babban zaben shekarar 2019 da sauran zabukan dake tafe. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China