Wasu mahara sun kaddamar da wasu hare haren kunar bakin wake kashi uku da yammacin ranar Lahadi, a sassan birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya sabbaba rasuwar mutane 16, baya ga wasu 18 da suka ji raunuka.
Mahari na farko dai rahotanni sun bayyana cewa namiji ne, wanda ya tada abun fashewa a wata tashar mota dake wajen birnin na Maiduguri, inda nan take ya hallaka mutane 13 tare da jikkata wasu mutane 5.
Da yake karin haske game da aukuwar lamari, kwamishinan 'yan sanda jihar ta Borno Damian Chukwu, ya ce bayan aukuwar harin na farko, wasu mata 'yan kunar bakin wake sun tada ababen fashewa dake daure a jikin su a wasu wuraren biyu dake birnin na Maiduguri, suka kuma kashe mutane 3, baya ga wasu da su ma suka ji raunuka sanadiyyar hakan.
A cewar Mr. Chukwu tuni 'yan sanda suka fara bincike game da aukuwar wadannan hare hare.
Ana dai zargin kungiyar Boko Haram da kitsa wannan ta'asa.(Saminu Alhassan)