Taron ya samu halartar wasu manyan jami'an kasashen Sin da Najeriya, ciki har da jakadan Sin dake Najeriyar, Mista Zhou Pingjian, da tsohon jakadan Najeriya dake Sin, Aminu Bashir Wali, da shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju, da mataimakin shugaban kwamitin kula da dangantakar Sin da Najeriya na majalisar wakilan Najeriya, Muhammadu Usman, tare kuma da mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar dattawan Najeriya, Shehu Sani.
Mahalarta taron sun kuma kalli bikin kaddamar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kafar talabijin.
A cikin jawabin da ya gabatar, jakada Zhou Pingjian ya nuna godiya ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, saboda sakon da ya aikewa takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, inda ya taya jam'iyyar kwaminis murnar shirya babban taron wakilanta karo na 19. Zhou ya kuma ce, kasar Sin aminiyar kasashen Afirka ce, haka kuma gwamnatin kasar Sin za ta yi kokarin aiwatar da manufofin da aka tsara a yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis a wannan karo, da ci gaba da martaba ra'ayoyin da shugaba Xi Jinping ya bayyana, wato nuna sahihanci da aminci yayin da take raya dangantaka da hadin-gwiwa da kasashen Afirka, a wani mataki na kara habaka dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya, har ma da nahiyar Afirka baki daya.(Murtala Zhang)