Kafafen yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa, shugabannin kasashen mambobin kungiyar sun amince da bukatar da kasar Moroccon ta gabatar na neman zama sabuwar mamba a kungiyar.
Morocco, wadda take matsayin 'yar kallo a kungiyar ECOWAS, ta gabatar da bukatar neman zama mambar ne a hukumance a watan Fabrairu, wata guda bayan da kasar ta zama mamba a kungiyar tarayyar Afrika AU.
Masarautar ta arewacin Afrika tana da kyakkyawar alaka mai karfi da kasashen yammacin Afrika. Ta kasance babbar mai zuba jari a yammacin Afrika, kuma ita ce kasa ta biyu mafi girma dake zuba jari a nahiyar Afrika.
A shekaru masu yawa da suka gabata, Morocco ta rattaba hannu kan daruruwan yarjejeniyoyi wadanda ke da matukar tasiri ga karfafa dangantaka a tsakanin kasashen mambobin kungiyar ta ECOWAS 15.(Ahmad Fagam)