Cikin wata sanarwar da ma'aikatar shari'a ta kasar ta fitar ya nuna cewa, a lokacin gudanar da bikin murnar darewarsa karagar shugabancin kasar a karo na 18, sarki Mohammed VI, ya amince da yiwa fursunoni kimanin 1,178 afuwa wadanda aka yi musu shari'a a kotunan kasar daban daban.
Sanarwar ta kara da cewa, daga cikin wadanda suka samu afuwar sarkin har da wasu daga cikin wadanda suka shirya zanga zanga a El Hoceima, a cewar sanarwar, an yi musu afuwar ne bisa la'akari da halin da iyalansu ke ciki da kuma mutunta dan adam.
Bisa la'akari da yadda al'amurra suke faruwa a Al Hoceima dake arewacin kasar Morocco, sarkin ya yi gargadin cewa, jam'iyyun siyasa da wakilansu suna kaucewa aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyansu, a wasu lokuta da niyya suke aikata hakan, a wasu lokuta kuma sakamakon rashin kwarewar aiki ko kuma rashin kishin kasa.
A cewar wata majiya daga mahukuntan kasar, kimanin mutane 176 ne aka damke su a lokacin gudanar da zanga-zangar.
Ana fuskantar zaman tankiya a yankin Al Hoceima ne tun a watan Oktoban shekarar 2016, tun lokacin da aka hallaka wani dillalin sayar da kifi Mouhcine Fikri, wanda aka kasha shi har lahira bayan 'yan sanda sun kama shi da laifin zarginsa da sayar da kifi marar inganci.
Masu fafutukar neman yiwa Fikri adalci a arewa maso gabashin yankin, sun yi ta yunkurin ganin gwamnatin kasar ta zuba jari mai yawa domin samar da karin ayyukan yi. (Ahmad Fagam)