Sarkin Morocco Mohammed VI, ya bayyana irin muhimmancin da nahiyar Afirka ke da shi a manufofin gwamnatin sa. Sarkin wanda ke jawabi yayin bikin cika shekaru 64 da juyin juya halin kasar sa, ya ce martaba makomar nahiyar Afirka batu ne dake da matukar daraja a gare shi, duba da yadda kasashen nahiyar suka kasance masu tarihi, da al'adu, tare da makoma ta bai daya.
Sarkin ya kara da cewa, Morocco na bin manufofin hadin gwiwa da sauran kasashen Afirka bisa kyakkyawar fahimtar ta ga nahiyar, tare da fatan gudummawar ta za ta share fagen cimma burikan nahiyar, karkashin manufar cin gajiya tare.
A shekarar 2017, Morocco ta sake komawa cikin kungiyoyin hadin kan Afirka bayan shekaru 33 da ficewar ta. Tuni kuma kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Ecowas ta amincewa kasar komen da ta nema.(Saminu Alhassan)