in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An mayar da bakin haure 'yan Nijeriya 138 gida daga Libya
2017-10-07 13:41:41 cri
MDD ta ce an mayar da bakin haure 'yan Nijeriya 138 gida daga Libya.

Shirin bada taimako na MDD dake aiki a Libya ya bayyana a jiya cewa, jimilar 'yan Nijeria 138 dake watangarari ne suka samu taimakon komawa gida bayan sun bukaci hakan da kansu, inda 70 daga cikinsu suka taba zama a cibiyoyin Trig al Seka da Tajoura da ake tsare 'yan cirani.

An mayar da mutanen gida ne karkashin shirin hukumar kula da 'yan cirani ta duniya.

Libya ta kasance hanyar da 'yan cirani ke bi inda suke fatan tsallake tekun Bahar Rum domin shiga Turai, saboda rashin tsaro da tashin hankali da ake fama da su a kasar, biyo bayan rikicin 2011 da ya hambarar da mulkin Mu'ammar Gaddafi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China