Babban lauya mai shigar da kara na ofishin atoney janar na kasar Al Seddiq Al-Sour, ya ce an bada umarnin kama mutanen da ake zargi 824 ne karkashin tsarin bincike da shigar da kararraki kan ayyukan ta'addanci da kuma barazanar tsaro, yana mai cewa an bada sunayensu a shingayen bincike dake kan iyakokin kasar domin daukar matakin da ya dace.
Ya kara da cewa, ita ma hukumar 'yan sanda ta duniya INTERPOL ta bada umarnin kame wasu daga cikin mutanen da ake zargi.
Al Seddiq Al-Sour ya ce an tattara sunayen ne yayin da ake bincike tare da kame wasu 'yan ta'adda a birane daban-daban na kasar. (Fa'iza Mustapha)