in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane sama da 20 ne suka mutu wasu kusan 200 kuma suka jikkata sakamakon tashin hankalin da ya auku a kasar Libya
2017-10-01 13:19:06 cri

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Libya ta bayar da labari a ranar 29 ga watan jiya cewar, dauki ba dadi a tsakanin dakaru na birnin Sabratha dake yammacin kasar Libya wanda aka yi har na tsawon makwanni biyu, ya haddasa mutuwar mutane 26, yayin da wasu 170 suka jikkata.

Mazauna birnin sun shaida cewa, yanzu an riga an dakatar da rikicin, amma har yanzu ana iya jin amon bindigogi a wasu lokuta.

A safiyar ranar 17 ga wata ne, wata motar dakarun da ke karkashin jagorancin kwamitin aikin soja na birnin Sabratha ta yada zango a wata tashar bincike ta rundunar sojojin yaki da kungiyar IS. Sakamakon kin amincewa da bincike da direban motar ya yi, an yi dauki ba dadi a tsakanin bangarorin biyu.

An kafa rundunar sojojin yaki da kungiyar IS ne a shekarar 2016, wadda take karkashin jagorancin gwamnatin sulhuntar al'ummar Libya, yawancin mambobinta sojoji ne na rundunar sojojin kasar. Rundunar tana zaune a birnin Sabratha, amma ba ta samu goyon baya daga wajen kwamitin aikin soja na birnin ba.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China