Majiyyata na kasa da kasa sun gayawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, wadannan mutane sun kunshi mata 22 da yara 4. Galibinsu sun fito daga kasashen Afirka dake kudu da Sahara. Suna son daukar jirgin ruwa domin zuwa kasashen Turai, amma jirginsu ya tsaya a yankin teku dake kusa da birnin Zawiyah sakamakon matsalar jirginsu. (Sanusi Chen)