in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da bakin haure 100 sun nitse a tekun Libya
2017-09-22 09:57:50 cri
Mai Magana da yawun sojin ruwan kasar Libya ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sama da 'yan ci rani 100 ne suka nitse bayan da jirgin ruwan dake dauke da su ya kife a tekun yammacin Libya.

Ayob Qasem ya bayyana cewa, 'yan cin rani sun nitse a tekun Zuwara, wanda keda tazarar kilomita 120 daga yammacin Tripoli babban birnin kasar Libyan, a lokacin da suke kokarin haurewa zuwa kasashen turai.

Jamai'an gudanarwa a tekun na Zuwara sun yi nasarar ceto mutane 7 ne da ransu a wani komi a wajen mai tazarar kilomita 20 daga tekun, inji Qasem.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China