in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaftarewar kasa ta yi sanadin mutuwar mutane 28 a kudancin Congo(Kinshasa)
2017-08-30 10:23:57 cri

Mutane 28 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon zaftarewar kasa da ta faru jiya Talata a birnin Kolwezi, babban birnin lardin Lualaba da ke kudancin kasar Congo(Kinshasa).

Gwamnan lardin Lualaba Richard Muyej ya tabbatar wa kafofin yada labaru cewa, mutane 28 ne suka halaka sanadiyar zaftarewar kasa a wurin hakar ma'adinai na wani kamfanin ketare dake aikin hakar ma'adinai a birnin. Da alamun yawan wadanda suka mutu sanadiyar bala'in na iya karuwa.

Haka kuma, mista Muyej ya ce, masu aikin ceto suna gudanar da aiki a wurin hakar ma'adinan, a kokarin kubutad da wadanda suke da sauran numfashi, amma har yanzu akwai wadanda kasa ta binne, ko da yake an yi nasara tono wasu gawawwakin wadanda suka mutu.

A ranar 17 ga wata ne, gangarowar kasa daga saman tsaunuka a lardin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar ta Congo(Kinshasa), inda mutane a kalla 200 suka rasa rayukansu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China