in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a zabtarewar kasa a Congo ya karu zuwa 200
2017-08-20 12:23:00 cri
Yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar tsagewar kasa ya karu zuwa mutune 200 a ranar Alhamis a kauyuka uku a lardin Ituri, dake arewa maso gabashin jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC.

Mataimakin gwamnan lardin, Pacific Keta, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Asabar cewa, jami'in shi ne ya zagoranci hadaddiyar tawagar MDD zuwa yankin da lamarin ya auku, yankin yana da wahalar shiga sakamakon manyan tsaunuka da ya addabi kauyukan, kuma akwai matsalar rashin kayayyakin aiki wanda hakan ya haifar da matsala wajen samun damar shigar jami'an aikin ceto zuwa yankin.

Mataimakin gwamnan ya ce, tun tuni ya ba da umarnin tura jami'an aikin ceto zuwa wajen da lamarin ya auku, amma a cewarsa, da wuya a iya samun wani mutum da ya tsira da ransa a inda al'amarin ya faru.

Keta ya ce har yanzu akwai abubuwan da ake bukatar yi a wajen, saboda har yanzu akwai mutane masu yawa dake binne a cikin laka. Ya ce suna bukatar taimaka na cikin gida da na kasa da kasa domin taimakawa dubban mutanen da lamarin ya shafa, kamar mutanen da suka rasa matsugunansu, da mata da kananan yara, wadanda ba su da abinci a sanadiyyar ibtila'in. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China