Da safiyar yau Talata ne aka rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 bayan shafe mako guda ana gudanar da taron a nan birnin Beijing. Gabanin kammalar sa, an zabi sabbin mambobin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadanda suka hada da mambobi 204 ciki hadda Xi Jinping da kuma mambobin dake jiran gado 172, tare da sabbin mambobi 133 na kwamitin tsakiya na ladabtarwa na jam'iyyar.
A gun taron, an zartas da kuduri game da rahoton da Xi Jinping ya gabatar a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar karo na 18, an kuma maida rahoton a matsayin sanarwar siyasa da ka'idojin gudanar da ayyukan da jama'ar kasar Sin za su bi, yayin da suke raya tsarin mulki na gurguzu, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Kaza lika an zartas da kudurin amincewa da nasarorin da kwamitin tsakiya na ladabtarwa na jam'iyyar karo na 18 ya samu a fannin yaki da cin hanci da rashawa.
Har wa yau an amince da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin jam'iyyar, wanda aka sanya "Tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki" a matsayin jigon zartas da muradun JKS, wanda aka tabbatar a matsayin muhimman ka'idojin jam'iyyar, tare da tunanin Marx da Lenin, da tunanin Mao Tsedong, da ka'idojin Deng Xiaoping, da manyan tunani na wakilci a fannoni 3, da ma akidar samun bunkasuwa bisa kimiyya da fasaha. (Zainab)