in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaman rufe babban taron JKS, inda za a zabi sabon kwamitin tsakiya
2017-10-24 09:33:32 cri
Da safiyar yau Talata agogon Beijing ne aka fara zama domin rufe babban taron JKS na 19, inda za a zabi sabon mambobin kwamitin tsakiya da na hukumar tsakiya mai tabbatar da da'a.

Ana sa ran wakilai za su zartar da kuduri game da rahoton kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 da na hukumar tabbatar da da'a tare da yi wa kundin tsarin jam'iyyar gyaran fuska.

An bude taron dake gudana bayan shekaru 5 a ranar 18 ga watan nan, a muhimmin lokacin da kasar Sin ke kokarin gina al'umma mai matsakaicin ci gaba a dukkan fannoni, a kuma wani muhimmin mataki, yayin da tsarin gurguzu na musamman mai sigar kasar Sin ya shiga sabon zamani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China