Kamar yadda za a zabe su tare da sauran sabbin mambobin hukumar siyasa a yayin taron farko na sabon kwamitin tsakiyar JKS karo na 19, sabbin manyan shugabannin zaunannen kwamitin hukumar siyasa za su gana da manema labarai na gida da na waje a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing da misalin karfe 12 sauran kwata na safe.
Za a nuna ganawar kai tsaye ta kafofin talabijin da rediyo na kasar Sin da kuma yanar gizo. (Ibrahim Yaya)