Tun a lokacin babban taron wakilan JKS karo na 18, jam'iyyar ta cimma nasarori da dama wajen jan ragamar harkokin jam'iyya, baya ga wasu tarin darussan da ta koya gami da wasu manyan nasarori da ta cimma, wadanda suka zama wajibi a sanya su a cikin kundin tsarin jam'iyyar a wannan lokaci, kana suka kasance wani bangare na dokokin jam'iyyar.
Kundin tsarin jam'iyya ya kuma bayyana cewa, wajibi ne jam'iyyar ta sam sanya –ido tare da daukar matakai na doka a dukkan fannoni.
A jawabin da ya gabatar yayin bude babban taron wakilan JKS karo na 19 a ran 18 ga watan, Xi Jinping ya bayyana "cin hanci" a matsayin babbar bazaranar da jam'iyyar take fuskanta.
A don haka ya ce, JKS za ta yi amfani da doka waje bankado masu aikata wannan danyen aiki da nufin hukunta su. (Ibrahim Yaya)