A yayin ganawar, gidan rediyon kasar Sin CRI, zai watsa labarai game da bikin kai-tsaye cikin harsunan Sinanci, da Turanci, da kuma Rashanci. Baya ga kafar rediyo, za'a iya sauraren shirin ta kafar sadarwar zamani wato Internet, ciki har da shafin www.cri.cn na harsunan Sinanci, da Turanci da kuma Rashanci. Bugu da kari, za'a iya kama shirin ta manhanjar wayar salula ta CRI, wato ChinaRadio.
A dayan bangaren kuma, gidan rediyon CRI zai watsa shirin kai-tsaye cikin harsuna 40, ciki har da Hausa, da Sinanci, da Turanci, da Larabci, da Swahili, da Pashto, ta shafin sada zumunta na Internet, wadanda suka hada da Facebook, da Twitter, da WeChat, da Weibo, da manhanjar wayar salula ta ChinaNews, da ChinaTV da sauransu. (Murtala Zhang)