in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 sun gudanar da zama na uku da na hudu
2017-10-23 19:40:59 cri
A daren ranar 22 da safiyar ranar 23 ga wata, shugabannin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, suka gudanar da zama na uku da na hudu a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing, inda suka zartas da daftarin jerin sunayen mambobin kwamitin tsakiya na jam'iyyar karo na 19, da mambobin dake jiran gado, da kuma membobin kwamitin ladabtarwa na tsakiya na jam'iyyar, wanda za a mika shi ga tawagogin wakilan jam'iyyar na larduna daban daban don tattauna kan shi.

Babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya shugabanci zaman biyu.

A ganin wakilan jam'iyyar, an fidda jerin sunayen ne bisa ka'idoji na demokuradiyya a jam'iyyar, wadanda suka kunshi fitattun wakilai daga wurare da yankuna da hukumomi da sassa daban daban, an kuma zabe su ne cikin adalci da daidaito, kana jama'ar kasar suna nuna goyon bayan su matuka ga hakan. An dai tsai da wannan daftari ne bayan da aka yi bincike da tattaunawa sosai.

Za a yi zaben membobin a hukunce a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a safiyar ranar 24 ga wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China