in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin marasa aikin yi a kasar Sin ya ragu sosai
2017-10-23 12:05:57 cri

Ministan kula da tsaron al'umma na kasar Sin Yin Weimin, ya ce kasar ta samu daidaito a bangaren samar da aikin yi cikin shekaru 5 da suka gabata, inda kididdiga ta nuna cewa, adadin marasa aikin yi dake da ragista a birane ya ragu sosai.

Yayin wani taron manema labarai a wani bangare na taron JKS, Yin Weimin ya ce aikin nasara ce da aka cimma bayan an sha matukar wahala, la'akari da yawan jama'a da kuma yadda sauyin fasalin tattalin arziki ya yi tafiyar hawainiya.

Sanarwar da ma'aikatar ta raba yayin taron manema labaru ta ce, ya zuwa karshen watan Satumban bana, adadin marasa aikin yi da aka yi wa rajista a birane ya tsaya a kaso 3.95 bisa dari, mataki mafi kasa da ya taba kai wa cikin shekaru.

Ministan ya alakanta ci gaban da muhimmancin da JKS ta ba batun samar da aikin yi da kuma rawar da tsare-tsaren tattalin arziki da na kudi da sauye-sauye ke takawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China