in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'i: Najeriya za ta samar da makamashi marar gurbata muhalli
2017-10-18 09:27:27 cri
Wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ya bayyana cewa, kasar za ta samar da kashi 30 bisa 100 na makamashi marar gurbata muhalli kuma a farashi mai rahusa nan da shekarar 2030.

Ministan lantarki, ayyuka da gidaje na Najeriyar Babatunde Fashola, shi ne ya bayyana hakan a lokacin taron koli game da halin da Afrika take ciki a halin yanzu wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

An shirya taron kolin ne domin tattauna batutuwa da suka shafi tattalin arzikin Afrika da nufin bada gwamnatocin shawarwari game da irin muhimman manufofin da za su aiwatar domin cimma nasarar bunkasa tattalin arzikinsu.

Fashola ya ce a watan Mayun shekarar 2015, kasar na da karfin lantarki megawatts 2,690 ne, kuma kashi 85 bisa 100 na lantarkin ana samunsa ne daga iskar gas.

Ya ce wannan shi ne dalilan da suka sanya kasar ke shiga cikin mawuyacin hali da zarar aka samu karancin iskar gas ko kuma aka lalata bututun iskar gas din.

Tsohon gwamnan jahar Legas ya bayyana wa mahalarta taron cewa, wadannan dalilai ne suka sanya gwamnatin kasar take ta kokarin lalibo wasu karin hanyoyin da za ta samar da kashi 30 bisa 100 na makamashin wanda take burin cimma hakan nan da shekarar 20130.

A cewarsa, tuni gwamnatin kasar ta kulla yarjejeniyoyi 14 na samar da megawatts 1000 na lantarkin ta hanyar amfani da hasken rana. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China