in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nijeriya na farautar tsageru a yankunan gabar ruwan kasar
2017-10-14 12:19:56 cri
Rundunar sojin Nijeriya, ta ce ta tura dakarunta yankunan gabar ruwan kasar, domin farauta da magance ayyukan tsageru da suka yi kaurin suna da manyan masu aikata laifuka a maboyarsu.

Da yake jawabi a tsibirin Takwa na birnin Lagos, babban hafsan sojin kasar Lt-Janar Tukur Buratai, ya ce da zarar kudade sun samu, za a ga yawan dakaru a tsibirin da sauran sassan kasar kamar yadda umarnin yaki da laifuffuka na 2016 ya tanada.

Babban hafsan ya tunatar da cewa, kashin farko na aikin da ya gudana tsakanin watan Augusta da Satumban bara, a jihohin kudancin kasar da suka hada da Abia da Bayelsa da Cross River da Delta da Imo da Rivers ya samu gagarumar nasara.

Ya ce aikin ya rage ayyukan tsageru da fasa bututun mai da lalata maboyar masu satar mutane don neman kudin fansa tare da ceto wadanda aka sace da kuma lalata sansanonin kungiyoyin asiri da dai sauransu.

Lt-Janar Buratai ya ce nasarar aikin rundunar a wadancan jihohi ta tilastawa wasu bata gari komawa wasu sassan kasar, abun da ya sa za a sake fasalin yankunan da za a yi aikin cikin kashi na biyu.

Har ila yau, Babban Hafsan sojin ya ce ana aikin ne tare da sauran hukumomin tsaro domin kara kaifin basirar dakarun wajen yaki da laifuffuka a yankuna kasa da na ruwa tare da dorawa a kan nasarar da aka cimma a kashin farko. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China