in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kasashen Afirka sun taya murnar gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19
2017-10-22 13:21:17 cri
Yayin da ake gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19, wasu shugabannin kasashen waje da jam'iyyu da kungiyoyi sun mika wasika ko buga waya don taya murnar gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 19.

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, yana fatan jama'ar kasar Sin za su samu ci gaba karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping. Sin ta nuna goyon baya sosai ga kasar Zambia bisa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka da tsarin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wanda ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin Zambia. Yana fatan za a gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 19 cikin nasara, sa'an nan jama'ar kasar Sin za su ji dadin rayuwa.

Shugaban kasar Congo Kinshasa Josef Kabila ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, taron ya tabbatar da nasarorin da aka samu yayin da aka gudanar da ayyuka da dama a shekaru 5 da suka gabata bisa jagorancin babban sakatare Xi Jinping, inda za a tattauna kan manyan batutuwan dake shafar makomar kasar Sin. Wannan taro yana da muhimmanci sosai, babu shakka za a amfanawa jama'ar kasar Sin a nan gaba. Yana fatan za a gudanar da taron cikin nasara.

Shugaban kasar Comores Azali Assoumani, ya bayyana a cikin wasikarsa cewa, tun daga babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 18, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta Sin Xi Jinping ya jagoranci kasar Sin wajen yin kwaskwarima kan tsarin kasa da samun bunkasuwa yadda ya kamata, kasar Comores tana fatan za a gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 19 cikin nasara, da nuna girmamawa ga babban sakatare Xi Jinping. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China