Mataimakin kwamitin jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar Rasha, wato jam'iyyar dinkuwar kasar Rasha Sergei Zheleznyak ya bayyana cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana kokarin kafa tsarin buri daya na dan Adam, da gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da sa kaimi ga yin mu'amala a tsakanin kasa da kasa a fannonin tattalin arziki da al'adu, da kirkire-kirkire da tsaro da sauransu. a halin yanzu, kasar Sin tana kokarin tabbatar da shimfida zaman lafiya a duniya da yankuna, da kasancewa muhimmiyar abokiya ga kasashen duniya da dama.
Mujallar The Atlantic ta kasar Amurka ta bayar da sharhi mai taken "Sin tana kokarin sake gina duniya" cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" muhimmiyar shawara ce dake shafar kasashen duniya da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta gabatar. Bisa tsarin "ziri daya da hanya daya", cinikayyar dake tsakanin kasa da kasa zata taimaka wajen rage rikicin dake tsakanin kasa da kasa. Sharhin yace, kasar Sin tana kokarin taimakawa tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Manazarcin cibiyar nazarin manufofin diplomasiyya ta kasar Habasha Abebe Ehnert, ya bayyana cewa, Sin da Afirka suna da buri daya, manufofin da kasar Sin ta gudanar ga kasashen Afirka suna biyan bukatun bunkasuwar kasashen Afirka. Kasar Sin ta dauki alhakinta dake bisa wuyanta yadda ya kamata, kana ita ce kyakkyawar abokiyar kasashen Afirka. (Zainab)