in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta cimma mizanin tattalin aziki da take buri
2017-10-21 18:06:58 cri
Shugaban hukumar rayawa da fasalta kasa ta kasar Sin He Lifeng, ya ce kasar Sin na sa ran tattalin arzikinta zai kai ko ma ya zarce mizanin da gwamnatin kasar ke son cimmawa a bana na kaso 6.5.

He Lifeng, ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a wani bangare na babban taron wakilan JKS karo na 19 dake gudana.

Ya ce darajar alkaluman tattalin arzikin kasar wato GDP zai zarce Yuan trillion 80 kwatankwacin dala triliyon 12.1 a bana.

Jami'in ya kuma shaidawa manema labaran cewa, a bana, tattalin arzikin na ta samun tagomashi ba tare da wani tangarda ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China