in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan Boko Haram 15 a arewa maso gabashin Najeriya
2017-10-12 09:29:06 cri
Dakarun sojin Najeriya sun hallaka mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram15 bayan da suka dakile harin da 'yan ta'addan suka yi yunkurin kaddamarwa a yankin Gwoza dake jihar Borno arewa maso gabashin kasar, kakakin rundunar ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba.

Birgediya janar Sani Kukasheka ya ce, soja guda ya rasa ransa a lokacin harin.

Kukasheka, ya ce dakarun sojin sun dakile harin ne wanda 'yan ta'addan suka yi yunkurin kaiwa sansanin sojin dake yankin.

Ya ce sojojin sun yi amfani da makaman da suke da shi inda suka yi barin wuta kan mayakan wadanda suke dauke da manyan makamai, kuma sun yi galaba a kan 'yan ta'addan.

A cewarsa, da dama daga cikin 'yan tada kayar bayan sun tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu

Ana zargin 'yan ta'addan Boko Haram da hallaka mutane sama da dubu 20, wasu mutanen miliyan 2.3 kuma sun tsere daga gidajensu a Najeriyar, tun bayan fara kaddamar da hare haren mayakan a shekarar 2009. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China