Da yake jawabi a taron kwamitin kwararru da wanzar da tsaro na kasashen Afrika (CISSA), karo na 14 a birnin Khartoum, al-Bashir ya ce Sudan tana aiki tukuru karkashin wasu managartan tsare tsare da Afrika ta bullo da su don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan ta kudun.
Ya kuma nanata aniyar kasar Sudan na samar da kayayyakin tallafi ga mutanen da rikicin ya shafa a sabuwar yantacciyar kasar.
Shugaba al-Bashir ya ce, a shirye kasarsa take ta samar da tallafin jin kai ga jama'ar Sudan ta kudu kuma za su bude kofa domin ba da damar shigar da kayayyakin tallafi ga al'ummar kasar Sudan ta kudun. Kana ya kara da cewa, sun bude kofa ga 'yan gudun hijjirar Sudan ta kudun wadanda ke neman mafaka a kasar don ba su tsaro ga lafiyarsu. (Ahmad Fagam)