Babban sakataren Jam'iyyar Jubilee mai mulkin kasar Kenya, kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar Raphael Tuju ya bayyana cewa, Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta samu manyan nasarori, a aikin da take yi na karfafa biyayya ga akidun jam'iyya daga dukkan fannoni, don haka ya kamata Jam'iyyar Jubilee ta koyi fasahohin da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta samu a fannin kara sanya ido kan harkokin jam'iyya.
Mr. Tuju ya fadi haka ne, yayin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a kwanan baya, inda ya kara da cewa, karfafa biyayya ga akidun jam'iyya na da nasaba da makomar jam'iyyar da ma kasa baki daya. Ya ce ganin yadda Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke gudanar da harkokin kasa, muna da yakinin cewa, duk kasar dake son samun wadata, da hadin kan al'umma, gami da zaman karko, dole ne ta samu wata jam'iyya mai mulkin kasa mai matukar karfi. Kuma kamata ya yi jam'iyyu masu mulki na kasashen Afirka daban daban ciki har da Jam'iyyar Jubilee, su koyi da fasahohin da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta samu, a fannin karfafa biyayya ga akidun jam'iyyar daga dukkan fannoni.(Kande Gao)