in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan tattalin arzikin kasar Sin a watanni 9 na farkon bana ya karu da kashi 6.9 cikin dari bisa makamancin lokacin bara
2017-10-19 13:39:03 cri
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da wasu alkaluma a yau dake nuna cewa, yawan GDP na kasar Sin a watanni 9 na farkon bana ya karu da kashi 6.9 cikin dari bisa makamancin lokacin bara, saurin bunkasuwarsa ya karu da kashi 0.2 cikin dari. Yawan GDP na kasar Sin tun daga watan Yuli zuwa Satumba na bana ya karu da kashi 6.8 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, karuwar ta tashi daga kashi 6.7 zuwa 6.9 cikin dari a watanni 12 a jere, kuma bunkasuwar na tafiya cikin sauri.

Kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin Xing Zhihong ya bayyana cewa, tattalin arziki na Sin ya bunkasa a watanni 9 na farkon bana kana yanayin tattalin arziki na gudana yadda ya kamata, ana kuma kara samun ci gaba a sabbin fannonin tattalin arziki, da kara samun moriya, da kuma kiyaye samun bunkasuwa yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China