in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan karuwar tattalin arziki ya kai kashi 6.9 cikin dari a watanni uku na farkon bana
2017-04-17 13:43:56 cri
Hukumar kididdigar kasar Sin ta fidda wasu alkaluma a yau Litinin, wadanda suka nuna cewa, yawan kudin da aka samu daga sarrafa arzikin kasa wato GDP na kasar Sin a watanni uku na farkon shekarar nan da muke ciki, ya kai RMB biliyan 180,68.3, adadin da ya karu da kashi 6.9 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara. Cikin wannan adadi kuwa, an samu karuwar kashi 3.0 cikin dari a fannin ayyukan gona, da kashi 6.4 cikin dari a fannin ayyukan samar da kayayyaki, da kuma kashi 7.7 cikin dari a fannin ayyukan samar da hidimomi.

Kakakin watsa labaru na hukumar Mista Mao Shengyong, ya ce ana ci gaba da samun ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata, kamar yadda ake samu tun bayan karshen rabin shekarar da ta gabata, kuma ana ta samun kyautatuwa a fannin.

Baya ga haka, muhimman alkaluman tattalin arziki sun wuce hasashen da aka yi, wanda hakan ya bude wani sabon shafi a bana, tare kuma da aza harsashi mai nagarta wajen cimma burin ci gaba a dukkan shekarar ta bana. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China