Shugaban hukumar kididdigar kasa ta Sin Ning Jizhe ya bayyana cewa, a shekarar 2016, an fuskanci kalubaloli wajen raya tattalin arzikin kasa da kasa, sakamakon hakan, kasar Sin ta yi tsaiwa tsayin daka kan sabbin manufofinta na neman bunkasuwa, domin tinkarar kalubaloli yadda ya kamata, yayin da take kara karfin bunkasuwar zamantakewar al'ummar ta. (Maryam)