Bisa ga sakamakon farko na zaben, wanda hukumar Kantar Sofres-onepoint pollster ta kasar ta fitar ya nuna cewa, jam'iyyar LREM ta lashe kujeru 315, sama da kujeru 289 da ake bukatar samunsu daga cikin adadin kujerun majalisar dokokin kasar 577.
A hannu guda kuma, jam'iyyar Conservatives ta lashe kujeru 133, inda hakan ya bata damar zama babbar jam'iyyar adawa a kasar. Sai dai kuma, 'yan jam'iyyar Republicans ba za su iya haifar da wata barazana ga gwamnatin Macron ba.
Jam'iyyar National Front (FN) ta dan samu ci gaba bayan da ta kwace kujeru 6 idan aka kwatanta da kujeru 2 da take da su a halin yanzu, yayin da jam'iyyar Socialist mai barin gado, ta yi hasarar dukkan kujerunta 32. (Ahmad Fagam)