Ministan watsa labarai da al'adu na Najeriya Lai Mohammed shi ne ya yi wannan kiran cikin wani sharhi da ya rubuta mai take "Yaki da ayyukan ta'addanci a Najeriya" wanda aka wallafa ranar Alhamis a jaridar Washington Times ta kasar Amurka.
Ministan ya ce, Najeriya ba ta dade da yakar daya daga cikin kungiyoyin masu tayar da kayar baya a kasar ba, a don haka bai kamata a baiwa kungitar ta IPOB wata dama da za ta samu gindin zama ba. Ya ce ayyukan da kungiyar ke gudanarwa ne ya sa aka ayyana ta a matsayin ta ta'addanci. Inda take zama barazana ga mutanen da take wakilta, domin babu abin da kungiyar ta sanya a gaba illa batun neman ballewa.
Ministan ya jaddada cewa, gwamnati ba za ta sake yin kuskure ta bar wata kungiyar 'yan ta'adda ta kama wani yanki na kasar ba.
Idan ba a manta ba a ranar 20 ga watan Satumban wannan shekara ce, gwamnatin Najeriya ta soke kungiyar ta IPOB dake fafutukar neman 'yanci a kudu maso gabashin kasar. (Ibrahim Yaya)