in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan jami'anta a DRC
2017-10-11 09:59:14 cri
Kwamatin tsaron MDD ya yi Allah wadai da babbar murya game da harin da aka kaddamar ranar Litinin inda ya hallaka jami'anta biyu da kuma raunata wasu 18, wanda gamayyar kungiyoyi masu dauke da makamai a demokaradiyyar Congo DRC suka kaddamar.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mambobin kwamitin tsaron MDDr sun bayyana sakon ta'aziyya da kuma nuna alhini ga iyalan jami'an wanzar da zaman lafiyar 'yan kasar Tanzaniya da aka hallaka, da kuma jajantawa gwamnatin Tanzaniyar, har ma da hukumar wanzar da zaman lafiyar ta MDD dake DRC wanda aka fi sani da Monusco. Kana sun yi fatar samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka samu raunuka a harin.

Mambobin MDD sun yi Allah wadai da harin da aka kaddamar da nuna tsokana kan jami'an na Monusco wanda kungiyoyin masu dauke da makamai suka kaddamar, kana sun bukaci gwamnatin DRC da ta gaggauta gudanar da bincike domin bankado wadanda suka aikata laifukan don gurfanar da su gaban shara'a.

Kwamitin tsaron MDD ya bukaci dukkan kungiyoyin masu dauke da makamai a duk fadin kasar, da su aje makamansu kuma su sani cewa kaddamar da harin kan jami'an wanzar da zaman lafiyar tamkar aikata laifukan yaki ne karkashin dokokin kasa da kasa.

Shi ma sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan tawagar jamai'an na Monusco a lardin Kivu na arewa dake DRC. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China