in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bayyana ra'ayoyin gwamnatin kasar kan inganta tsaro a duniya
2017-10-07 12:57:19 cri
Shugaban sashen takaita yaduwar makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mista Wang Qun, ya bayyana wasu manyan ra'ayoyin Gwamnatin kasar Sin game da tabbatar da tsaro da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya.

A cikin jawabin da ya gabatar Jiya Jumma'a, a wajen babbar muhawarar kwamitin kula da harkokin kwance damarar soja da tsaron kasa da kasa na babban taron MDD karo na 72, Wang Qun ya ce, a halin yanzu ana fuskantar wasu manyan sauye-sauye da ci gaba tare kuma da sabbin kalubale a fannin tsaro a fadin duniya. A don haka, akwai bukatar kasa da kasa su bullo da sabbin dabarun inganta harkokin tsaro a duniya.

Jami'in ya ruwaito Shugaban kasar Sin Xi Jinping na bada shawarar kasa da kasa su yi hadin-gwiwa kafada da kafada, da neman ci gaba mai dorewa, a wani kokari na kafa sabuwar dangantaka tsakanin kasashen duniya, da dukkan kasashen za su mora. Wang Qun ya kara da cewa, wadannan ra'ayoyi na shugaba Xi Jinping, sun kafa wata alkibla ga yadda za'a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da lalubo hanyar da kasashen duniya za su bi wajen kiyaye zaman lafiya da tabbatar da kwanciyar hankali. Wang ya ce, kasa da kasa za su iya yin koyi gami da tallata wadannan ra'ayoyi na gwamnatin kasar Sin a fannin inganta yanayin tsaro.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China