Da yake tsokaci game da muhimmancin dake tattare da ajandar dawwamamman ci gaban duniya nan da shekarar 2030, babban jami'in MDD ya bayyana cikin wani sakon bidiyo don bikin tunawa da ranar kawar da talauci ta duniya cewa, wannan ajanda wanda duniya baki daya ta amince da ita, za ta samar da wata irin duniya mai cike da zaman lafiya da kuma kyautata rayuwar al'ummar dake rayuwar a duniyar da kare martabar al'ummar duniya baki daya.
Mista Guterres, ya bukaci a dauki matakan da za su dakile karuwar talauci domin kawar da wannan matsala baki daya daga doron kasa, kana idan ana son magance wannan matsalar, dole ne a saurari ra'ayoyin mutanen dake fama da talaucin, kuma a gudanar da aikin tare da su muddin ana son kawo karshen matsalar daga doron kasa.
Sama da mutane miliyan 800 ne ke fama da talauci a fadin duniya, kuma mutanen suna ci gaba da rayuwa ne cikin matsanancin talauci, kana wasu mutanen masu yawa kuma suna fama da barazanar karuwar rashin aikin yi, da rashin tsaro, da rashin daidaito, da kuma matsalar da suke fuskanta sakamakon sauyin yanayi. (Ahmad Fagam)