Rahoton JKS ya nuna cewa, ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya tushen siyasa ne na dangantakar da ke tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan. Ra'ayin bai daya da aka samu a shekarar 1992 wanda ya amince da wannan ka'ida, wani muhimmin abu ne da ya tabbatar da bunkasar dangantaka yadda ya kamata. Muddin aka amince da wannan ra'ayi na bai daya, to bangarorin biyu za su iya tattaunawa da juna, kuma ko wace jam'iyya da kungiya da ke yankin Taiwan, ba za ta gamu da cikas ba yayin cudanya da babban yankin kasar Sin. Rahoton ya kuma jaddada cewa, babban yankin kasar Sin na da aniya da kuma karfi sosai wajen murkushe duk wani yunkurin neman kawo baraka ga kasar Sin. (Kande Gao)